FITACCIYAR jaruma Maryam Isah Abubakar, wadda aka fi sani da Maryam Ceeter, ta yi aure a jiya Juma'a, 14 ga Fabrairu, 2020 ba tare da ta sanar da jama'a ba, ciki kuwa har da 'yan'uwan ta 'yan fim.

Mujallar Fim ta gano cewa an ɗaura mata auren ne da wani mai suna Alh. Isah Usman Babba da misalin ƙarfe 1 na rana a masallacin Juma'a na Alfurƙan da ke Alu Avenue a unguwar Nassarawa da ke cikin garin Kano, bayan an idar da sallar Juma'a.

Babu wani ɗan fim da ya halarta, sannan shi kan sa angon bai halarta ba.

Tun kusan wata ɗaya da ya wuce Maryam ta sanar da wakilin mu cewa ana ta yin shirin auren, amma dai ba a saka lokaci ba.

Ta yi alƙawarin cewa idan an saka lokacin, za ta sanar da mu. Hakan ba ta samu ba.



A wajen walima

Maryam cike da farin ciki a wajen wakimar auren ta
Sai bayan an ɗaura auren ne wani da ya halarci ɗaurin auren ya tabbatar wa da mujallar Fim cewa an ɗaura auren.

Maryam dai ƙanwa ce ga fitacciyar jaruma Mansurah Isah.

Wannan shi ne auren ta na uku.

Ɓoye ɗaurin auren da jarumar ta yi ba wani sabon abu ba ne a wajen 'yan Kannywood, musamman mata, domin kuwa har ma abin ya zama ruwan dare game duniya.

Mu na fatan Allah ya ba Maryam da angon ta mai sunan baban ta zaman lafiya da ƙaruwar arziki.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top