Intanet a yanzu ta zama Hantsi leka gidan kowa, da wahala ka iya samun gidan da ba a amfani da intanet alal a kalla ko da mutum guda ne.
Tana taka muhimmiyar rawa ta fuskar kasuwanci, binciken ilimi da kuma sada zumunci a tsakanin jama'ar duniya.
Kamar yadda take kawo ci gaba, a wasu lokutan takan haifar da matsaloli nan da can.
A kasashe irin su Najeriya ana zargin takan taka rawa wajen rushewar tarbiyayyar yara, musamman ta hanyar ba su damar ziyartar shafukan da ke yada hotunan bidiyon badala.
!0 ga watan Fabrairu ce ranar tsaftace shafukan intanet ta duniya.
Majalisar Dinkin Duniya ce ta ware ranar da zummar jan hankalin iyaye game da bibiyar shafukan da 'ya'yansu ke ziyarta, da kuma aniyar samar da kariya ga masu amfani da shafukan a duniya.
Abdullahi Baban Sadiq, wani masanin harkokin intanet ne a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa akwai wani wuri a intanet da ake kira (Black Hole), wani wuri ne da in ka shige shi kakan iya kare rayuwarka a ciki ba tare da ka fita ba, kamar mutum ne a ce ya fada rijiya gaba dubu.
''Su ne shafukan badala, da shafukan caca da kuma harkar damfara, inda ka sabawa kanka da shiga irin wadannan wurare to har tsufanka idan ba a yi hattara ba a haka za ka kare.''
Ya shaida mana wasu matakai biyar da masu mu'amala da intanet za su iya dauka don kaucewa hadarinta.

Be nice to each other onlineHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

1. Tsarin (Parental Control)
Yawancin kayayyakin fasaha a yanzu kan zo ne da wannan tsari, wata dama ce da aka bai wa iyaye domin bibiyar shafukan 'ya'yansu na sada zumunta da kuma iyakance wuraren da za su rika ziyarta a intanet.
A kasashen da suka ci gaba za ka tarar yawancin yara na da na'urorin kwamfuta da sauran kayayyakin fasaha, amma a can akwai damarmaki da yawa da iyaye ke da su na bibiyar al'amuransu.
Amma a kasashe irin su Najeriya dole sai dai ka rika daukar wayar kana dubawa.
2. A san wadanda suke abota da su
A shafukan sada zumunta kowa na da damar yin abota da kowa ba sai lallai wanda ka sani ko wanda ke garinku ko kasar da kake ba, in kuwa haka ne, kenan ba ka san wanda kake mu'amala da shi ba, mutumin kirki ne ko akasin haka.
Idan danka ya kulla abota da wanda ba na kirki ba wannan zai iya shafarsa, watakila ta hanyar koyon kutse ko damfara a intanet ko ma shafar dabi'unsa a rayuwar yau da kullum.
3. A wayar musu da kai game da intanet din
Yana da muhimmanci a wayar da kan yara, a nuna musu cewa intanet din nan fa na da nata matsalolin, ka da a bar su da tunanin cewa babu abin cutarwa tattare da ita, ta haka ne za su san cewa akwai abin da ya kamata su kauce masa.
Idan so samu ne ma a nuna musu irin wadannan shafuka a kuma nuna musu hadarinsu, maimakon su ji a wajen abokansu da watakila ba za su nuna musu cewa akwai hadari tattare da su ba.
4. A san inda suke shiga
Babu inda ba za ka iya shiga ba a intanet, in kuwa haka ne yana da kyau kasan inda 'ya'yanka ko danka ke shiga a irin wadannan miliyoyin shafuka, watakila sukan iya zama ba masu kyau ba, idan aka gano hakan da wuri akwai damar da za a ankarar da su domin su kauce musu, ko ma kwace wayar ko na'urar da suke amfani da ita idan akwai bukatar hakan.

5. A rika tattaunawa da yara

Ka rika tattaunawa da yaranka, tambaye su wace irin riba suke ci saboda amfani da intanet ne? Ina da ina suke shiga? Me ke ba su takaici a intanet?
Za ka fuskanci abubuwa da dama daga amsoshin da z aka ji daga gare su, za ka fahimci shin suna kyamatar shafukan badala ne ko kuwa?


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top