Daga Datti Assalafiy

Gwamnatin jihar Delta karkashin jagorancin gwamna Ifeanyi Okowa ta fara kaddamar da yunkurin rushe wani Masallacin 'yan uwanmu musulmai da ake ginawa a unguwar Kiogbodo dake karamar hukumar Burutu.

Wannan abin na faruwa bayan gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya rushe masallacin 'yan uwa Musulmi dake Trans Amadi Port-harcourt.

Hakika wannan sabon salo da wasu wawayen shugabannin kudu maso kudancin Nigeria suka fito dashi na rushe Masallacin Musulmai abin takaici ne da bacin rai, so suke su haddasa wata sabuwar fitina a cikin kasa wanda ba zasu taba cin nasara ba Insha Allah.

Sai dai abinda suka kasa fahimta shine, Musulmai masu son zaman lafiya ne, ba za'a biye musu ba, ko da masallaci ko babu Masallaci, ko a tsakiyar tsananin zafin rana ko tsananin saukar ruwan sama Musulmai zasu yi ibada mu bautawa Allah Ubangijinmu.

Amma tunda akwai doka na gwamnatin  Nigeria da ya bawa kowa ikon yin bauta da yin addinin da yaga dama a ko'ina yake a fadin Nigeria, zalunci ne a tauye wa musulmi hakkinsu na gina dakin ibada, idan zai kasance akwai coci a garin Mujaddadin Musulunci to bai kamata ace an haramta wa Musulmai gina masallaci a kudu maso kudancin Nijeriya ba.

Musulunci shine addinin da ya karantar damu girmama dakunan bauta, ko yaki ake tsakanin Musulmai da kafurai, sai musulmai suka biyo kafurai, idan kafurai suka shiga dakin bautarsu to sun tsira, musulunci bai ce a bi su cikin dakin bautarsu a yake su ba, saboda yadda musulunci ya ke girmama dakunan bauta.

Kamar yadda muka goyi bayan 'yan uwa Musulmai na jihar Rivers cewa su kwantar da hankali, su bi matakin dokar Kasa, to yanzu ma muna goyon bayan 'yan uwa musulmi na jihar Delta da su kwantar da hankalinsu, su bi matakin doka wajen kwato hakkinsu.

Yaa Allah Ka daukaka Musulunci da Musulmai.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top