Mutumin nan dan kasar Italiya da ya fara shigowa da cutar Coronavirus Najeriya ya bayar da gudunmawar jini ga hukumomin lafiya a jihar Legas.

 

 

Mutumin ya bayar da nau’in kwayoyin halittar jini ne da ake kira plasma wanda shi ne ruwan da ke daukar sinadarin da gina jiki da sauran sinadaran da ke jinin. Kwayoyin halittar plasma na mutumin dai na dauke da sinadarin da ke yakar Coronavirus.

 

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu, wanda ya sanar da hakan, ya ce jami’an kiwon lafiya na jihar da na jihar Ogun tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya suka yi aikin kula da lafiyar mutumin har Allah Ya sa ya warke, aka sallame shi cikin farin ciki yayin da yake cike da koshin lafiya.

 

Mista Sanwo-Olu ya kuma ce zuwa yanzu an daskarar da nau’in jinin a dakin ajiya na asibitin da ke kula da wadanda suka kamu da cutar a Yaba, za kuma a yi amfani da shi wajen yi wa wadanda suka kamu magani.

 

 

Jami’an kiwon lafiyar da suka kula da mutumin sun dauki hoto tare da shi a lokacin da za a sallame shi inda ake iya ganinsa a cikin hoton sanye da gajeren wando, sai dai an rufe fuskarsa ba a kuma bayyana sunansa ba domin ba shi kariya.

 

 

Dan kasar Italiyar ya zo Najeriya ne ranar 24 ga watan Fabrairu daga birnin Milan inda aka ba da sanarwar ya kamu da cutar a ranar Alhamis 27 ga watan.

A daren ranar Juma’a ne dai jami’an kiwon lafiya a jihar ta Legas suka sallami dan kasar Italiyar bayan ya warke daga cutar.

Aminiya.



© hutudole

Post a Comment

 
Top