Hukumar Kula da zirga-zirgar a baban hawa dake babban birnin tarayya Abuja ta umarci jami’anta dake aikin kula da zirga-zirgar ababen hawa a duk fadin garin, da su kame direbobin da ke daukan fasinjoji da suka wuce ka’ida.

Shugaban wanda ke kula da harkokin zirga-zirgar ababen hawa, Mista Ikharo Attah ne ya bayyana hakan ranar Lahadi a Abuja yayin wata tattaunawa da manema labarai.

Ya ce a daidai lokacin da duniya ke yakar cutar Coronavirus ta hanyar ba da shawara wajan rage cudanyar jama’a ba daidai bane ga direbobi su cika motocin su makil don neman kuɗi cikin sauri.

Ya ce; “Wadanda ke dauke da fasinjoji biyu a gaban motocin su za a dauki mataki akan su tare da kwace lasisin tukinsu. a cewar sa baya ga hatsarin kiwon lafiya, shima kansa direba a takure yake ta yadda bazai iya yin walwala ba a yayin da yake tuki.

Ya kara da cewa suma za a duba manyan direbobi yanayin lodin Kayan su da kyau don tabbatar da cewa ba sa cika motocinsu.

Attah, ya kuma yi kira ga masu amfani da hanyoyin sufuri musamman wadanda aka ba su izinin yin aiki a yankunan karkara kamar babura masu kasuwanci da kuma tricycle da suma su guji yin cunkoso.

A karshe yayi kira da a rage cunkoso da ya kai mutane 50 a tashoshi, inda kuma yayi Kira da ai gaggawar kiran hukuma ga wanda aka samu ya kamu da cutar.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top