Kasancewar ta fitacciyar ma rubuciya da take tashe tsawon lokaci a masana’antar Kannywood, Fauziyya D Suleiman tsohuwar marubuciyar litattafan Hausa ce wadda daga baya ta fara rubutun fina finan Hausa. A tsawon shekaru ta rubuta manya manyan fina finan da su ka yi tashe a masana’antar.

Ba ya ga sunan da Fauziya ta yi a fannin rubutun litattafai da na fina finan Hausa, ta kasance kuma mai gabatar da shirin tattaunawa da masana domin wayar da kan mutane a kan rayuwar duniya a tashar AREWA24.

A ‘yan shekarun nan ne Fauziyya ta bazama wajen taimakawa marasa galihu da marasa lafiya da nakasassu ta hanyar amfani da shafinta na dandalin soshiyal midiya wajen shelanta bukatu na mutane da ke neman taimako, kuma ta kan bi diddigin ganin cewar taimakon da mutane su ka bayar an amfanar da shi ta yadda ya kamata. Hakan ya sa Fauziyya kasancewa zakarar gwajin dafi da masana’antar Kannywood a kan harkar taimako.

Ko da ya ke ba Fauziyya kadai ce a masana’antar da ke aikin taimako irin wannan ba, akwai mutane irinsu Mansura isah, Hadiza Gabon, Halima Atete da dai sauransu, amma saboda yawan taimako a kai a kai da Fauziyyar ke yi ya sa ta yi fice a kan wannan harkar, har ya kai ta ga bude gidauniya mai suna TODAYS LIFE FOUNDATION domin hassasa wannan aiki na ta na taimakawa jama’a.

A zantawar da ta yi da wakiliyar mu ta bayyana mata cewar ta fara da marasa lafiya ne inda take dora hotunan marasa lafiya a shafinta na soshiyal midiya wadanda ba za su iya sayawa kansu magani ba ta nema musu taimako a wajen al’umma. Daga baya ta qara da ciyar da marayu mabuqata da marasa galihu, da kuma samar da sutura da ilimi ga marayu.

Ko me ya sa ta fara wannan aiki? Ita ce tambayar da mu ka yi mata.

“Dalilin wani bawan Allah matashi mai suna Nayeef, Ladani ne a wani massallaci da ke Fagge a jihar Kano, wanda ya kamu da cutar Koda ya sa na fara nema wa mutane marasa hali taimako.

Wata rana ina kan Facebook a shekarar 2016 naga an saka hoton yaron ana neman taimako Za'ayi masa wankin Koda babu  kudin yin wannan wankin, ni kuma nasan shi mutum ne mai kula da addini hasali ma mahaddacin Alqur`ani ne.

Hakan ya sa na dauki wannan hoton nashi da aka saka bayan na yi bincike na tabbatar da lallai ya na bukatar taimakon, na yi kira ga jama'a akan cewa su taimaka ma sa. cikin Ikon Allah ina sakawa a shafina na Instagram muka fara samun tallafi da ga wajen mutane daban daban.

A haka har labarin ya je kunnen mai martaba Sarkin Kano Alh Muhammad Sunusi na ll ta dalilin wata kawata wadda ta ke aiki a fadar Sarkin, a nan take Sarkin yace ya dauki nauyin kula da shi har Allah ya bashi lafiya.

Ganin haka ya sa  mutane suka fara biyo ni ta shafina na Instagram su na yi mun magana akan su ma a taimaka musu su na da marasa lafiya. Ni kuma Sai na dauki hoton mara lafiyan nasu Sai na daura a shafin nawa tare da lambar su da kuma lambobin asusun su na banki.

Ana cikin haka sai mu ka samu matsala da wani mutumi wanda ya roka aka tara mai kudi dan a  taimaki yar shi za'a yanke mata kafa, sai ya ki bayar da Kudin da aka tara domin yiwa yar aiki har ya bari ciwo yayi ta cin jikin yarinyar. Bayan anyi wata biyu sai mahaifiyar yarinyar ta kirani tana kuka akan cewa  a taimaka mata, mu kuma bayan an tura masu kudi tuntuni Sai na ce mata wancan Kudin da aka basu na taimakon fah? Sai tace wallahi wancan Kudin da aka bayar mijin nata guduwa yayi bai bayar da wannan Kudin ba."

Fauziyya ta kara da cewa “Ni kuma sai hankali na ya tashi tunda ba bibiyar lamuran mu ke yi ba idan kawai mun roka anyi shi Kenan, na ce mata toh ya akayi haka tace ganin Kudin yayi yawa ya sa ya gudu ya kasa fitarwa, ana cikin haka muka nemo mijin bayan ya kashe Kudin duk.

Wannan dalilin yasa na bude gidauniya da kuma asusun da za'a rika zuba kudaden taimako idan an samu marasa lafiya, daga nan kawai ni da wasu abokan aikina muka fara zuwa asibitin da kanmu anayin komai a idon mu dan gujewa irin waccan matsalar”.

Marubuciyar ta ce basu taba samun wani taimako na musamman da ga Gwamnati ba amma su na samu k

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top