Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi
Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano
Daya daga cikin jarumai mata da suka yi tashe a baya mai suna Sapna Aliyu wadda a yanzu aka dauki lokaci mai tsawo ba tare da ana ganin ta a cikin harkar ba a wannan lokacin, ta bayyana rashin ganin nata a matsayin wani abu da ya shafi al'amari na kashin kanta ba wai don an daina yayin ta ko kuma harkar ta ajiye ta ba.
Jarumar ta bayyana haka ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilin mu Mukhtar Yakubu, a kan rashin ganin nata da ba a yi tsawon lokaci in da take cewa"
To gaskiya ne na dan samu lokaci ba a gani na a harkar fim kuma har ma wasu na ganin kamar ko a yanzu an daina yayi na ne, to gaskiya ba haka ba ne, domin duk Wanda ya san Sapna Aliyu Maru a cikin harkar fim ya san ba a daina yayi na ba har yanzu ana yayi na a cikin harkar fim, kawai dai a yanzu na kara fadada harkoki na ne na kasuwanci, Inji ta.
Ta cigaba da cewa dan haka sai ya kasance ba na samun zama sosai saboda tafiye tafiye da na ke yi na harkar kasuwanci, don a yanzu na fi mayar da hankalina wajen kasuwanci ka ga ina fita waje ina sayo kayayyaki kamar su atamfofi da yadika da takalma, wannan yasa na tattara hankali na a kan harkar domin na samu na gina ta.
Safna, ta kara da cewa kuma idan na dawo ina kanti na ko ina wajen raba kaya ko hada kudin kayan, ka ga ina harkar fim za ta yiwu a irin wannan yanayin?
Sannan ta Ce, su masu ganin kamar ta kare min ne, sam ba haka ba ne, saboda ni da kudi na nake gudanar da harkar fim, kowa ya san ni furodusa ce, na shirya finafinan da yawa da kudi na kuma har yanzu ina da kudi masu yawa a kasuwa don haka ai ba ta kare mini ba, inji ta.
Kuma har yanzu ina samun gayyatar mutane idan za su shirya fim su kan so na fito a cikin fim din su, to sai dai ba ni da lokaci ne, kuma ni kaina ina son na samu lokaci na rinka fitowa, domin kuwa harkar fim ce ta daga daraja ta a duniya har na samu matsayin da nake, don haka ina alfahari da harkar fim, inji Safna.
Da muka tambaye ta ko yaushe za ta dawo ta ci gaba da harkar fim?
Sai ta ce" to ni daman ba tafiya na yi ba ina nan a ciki, don haka ko yanzu na samu lokaci zan ci gaba ne, kuma ko a yanzu da aka yi rajistar 'yan fim a Hukumar tace finafinai ai na je na yi a matsayi na na furodusa, don na san nan gaba zan yi furodusin din wasu finafinai da nake da su don haka har yanzu ina cikin harkar fim wasu harkoki ne suka sa ba a gani na.
Daga karshe dai jarumar ta yi godiya ga dumbun masoyan ta da suke tuna ta har suke tambayar ta a sakamakon rashin ganin nata don haka ta yi fatan Allah ya bar ta da masoyan na ta.
Hakkin Mallaka, Jaridar Dimokuradiyya.
©HausaLoaded
Post a Comment